Connect with us

News

Rundunar ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 1,284 Da Ake Zargi Da Aikata Mabambanta Laifuka

Published

on

DAGA YASIR SANI

Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce dakarunta sun sami nasarar kama mutane 1,284 da ake zargi da aikata mabambanta laifuka a cikin makwannin shidda da suka gabata.

Advertisement

Mai Magana da yawun hukumar na kasa Muyiwa dejobi ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a yayin da ake holen wadanda ake zargin da aikata laifuka daban daban.

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu Da Aka Dawo Da Shi Kwanan Nan Ya Koma Jam’iyyar APC A Hukumance.

PRNigeria ta ruwaito cewa daga cikin wadanda aka kama akwai mutum 307 da ake zargin su da aikata fashi da makami sai kuma 296 da ake zargi da aikata laifukan garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, sai kuma mutane 176 da ake zargi da laifukan fyade da tabargaza, ana kuma zargi mutane 301 da aikata laifukan kisan kai, sai kuma mutane 204 da ake zargin su da shiga kungiyoyin asiri.

Advertisement

Adejobi yace rundunar ta sami nasarar kubutar da mutane 97 da akayi garkuwa da su, inda suka sami nasarar kwato makamai 284 gami da alburusai 6,702.

 

Advertisement

PRNigeria Hausa

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending