Connect with us

News

Muhimman Abubuwa Shida Dangane Da Tababar Da Ta Barke Tsakanin Dangote Da Gwamnatin Shugaba Tinubu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Duk mai sauraron kafafen yada labarai ko bibiyar dandalin sada zumunta ya san da tirka-tirkar da ta kunno kai tsakanin gwamnatin tarayya da hamsahakin dan kasuwa, Aliko Dangote, a kan matatar sa ta man fetur.

Jaridar INDA RANKA ta bibiyi musayar yawun da ta barke tsakanin Dangote da kamfanin NNPCL da kanwarta hukumar NMDPRA mai kula da harkokin da suka shafi man fetur da kuma muhimman abubuwan da suka biyo baya.

Advertisement

Allah Yasa Zanga-Zangar Da Za A Yi Ta Kawo Ƙarshen Gwamnatin Shugaba Tinubu – Sheikh Murtala Bello

1. Kalaman Dangote: Tun bayan sanar da kaddamar da matatar mai ta Dangote a watan Janairu, shugaban rukunin kamfanunuwan Dangote, Aliko Dangote ya yi zargin cewa akwai wasu manyan masu kudi a bangaren kasuwancin mai, a ciki da wajen Nigeria, da suke kokarin ganin matatar sa bata cimma burinta na fara tace danyen mai a Nigeria ba kamar yanda Jaridar WIKKI TIMES ta ruwaito.

Yayin da yake bayyana irin kalubalen da sabuwar matatar sa ke fuskanta, Dangote ya ce; sharrin manyan ‘yan kasuwar Mai na duniya ya fi na manyan dillalan kwaya.

Advertisement

 

2. Kalaman shugaban NNPCL: A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana cewa shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana cewa matar man fetur ta kasa dake Fatakwal, jihar Ribas, zata fara aiki a watan Agusta, ta Kaduna da Warri kuma zasu fara aiki a Disamba, yana mai jinjina cewa ‘ba karya muke ba‘.

Advertisement

 

3. Furucin shugaban hukumar NMDPRA: Farouk Ahmed, babban jami’in gudanarwa a NMDPRA, ya shaidawa manema labarai, a fadar shugaban kasa, cewa matatar Dangote bata da ingancin samar da mai tare da bayyana cewa har yanzu hukumar su bata bawa Matatar Dangote lasisin fara aiki ba.

Advertisement

 

A cewar Farouk, Fetur da sauran sinadaran da matatar Dangote ke samarwa basu da nagarta idan aka kwatanta da wadanda ake shigowa da su daga ketare.

Advertisement

 

Har ila yau, ya zargi Dangote da yunkurin mamaye harkar tace mai da siyar da shi a Najeriya tare da bayyana cewa Dangote ya nemi NNPC ta umarci dillalan mai su koma siyen fetur da gas a matatar sa, lamarin da ya ce ba daidai bane ta fuskar kasuwanci, kuma matar Dangote ba ta kammalu ba, da sauran aiki.

Advertisement

 

4. Martanin Dangote: Aliko Dangote ya fito ya mayar da martani ga kalaman Farouk inda ya nemi shugaban na NMDPRA ya fadi inda dakinsu na gwajin sinadaran mai yake sannan kuma ya gabatar da sakamakon gwajin sinadaran mai da gas na matatar Dangote domin tabbatar da abinda ya fada dangane da nagartar fetur da gas daga matar Dangote.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Kazalika, Dangote ya musanta batun cewa NNPCL ta mallaki kaso 20% na matatar sa tare da bayyana cewa zai siyarwa NNPCL matatar idan haka suke so.

Advertisement

Dangote bai tsaya nan ba, ya shaidawa manema labarai cewa tun farko sai da wani abokinsa attajiri ya bashi shawarar kai ya narka dukiyarsa a Nigeria saboda akwai matsaloili a tsarin gwamnati da kuma ‘yan hana ruwa gudu.

5. Zaman Sulhu: A ranar Litinin ne aka fara wata tattaunawa tsakanin Dangote da karamin ministan man fetur da shugaban NNPCL da sauran wasu shugabanni a bangaren harkokin mai domin kawo karshen dambarwar da ta kunno kai.

Advertisement

6. Ra’ayin jama’a: Tunda tirka-tirkar ta balle jama’a daga kowanne bangare na Nigeria suke bayyana mabanbanta ra’ayoyi.

Da yawan masu sharhi sun bayyana cewa akwai boyayyiyar badakala a kamfanin NNPCL da kasuwancin man fetur wanda fara aikin matatar Dangote zai tona asirinsu, musamman batun adadin litar danyen mai da ake haka kowacce rana a Nigeria da kuma batun biyan tallafi da gwamnati ta janye.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending