Connect with us

News

Zanga-Zanga: Gwamnatin  Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gwamnatin Jihar Yobe ta umarci dukkanin makarantun firamare da sakandare na jihar da a rufe su daga ranar 31 ga watan Yuli saboda zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan kan wahala da yunwa.

Advertisement

Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Abba Idriss, ya fitar tare da sanya hannun daraktan kula da makarantu, Bukar Modu a Damaturu.

An samu jagoran zanga zangar matsin rayuwa a unguwar tudun Yola dake Kano

“Mai girma kwamishina, Farfesa Abba Idriss Adam ne, ya umarce ni da na rubuto tare da sanar da ku amincewarsa na rufe dukkanin makarantun Firamare da Sakandare a jihar kamar yanda Jaridar Leadership ta ruwaito

Advertisement

“Duk da haka, bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa, makarantun jihar za su kasance a rufe daga ranar Laraba 31 ga watan Yuli, 2024,” in ji Modu.

Sanarwar ta kuma umarci makarantu da su koma gudanar da harkokin ilimi a ranar Lahadi 15 ga watan Satumba, 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending