Politics
Sanata Ndume Ya Nemi Afuwar Jamiyyar APC Bayan Ya Soki Shugaba Tinubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon babban mai shigar da kara a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya nemi afuwar shugabannin jam’iyyar APC mai mulki kan rashin tuntubar jam’iyyar kafin ya fito fili ya zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da gazawa Kan bukatun talakawa.
Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a zauren majalisar dokoki ta kasa, ya ce amman har yanzu fa Yana nana Kan maganarsa, na rashin Ko in Kula da gwamnatin Bola kewa Al,ummar nageriya inda ya jaddada cewa duk abin da ya fada to yayi shine sabida nuna kishin kasa sa
Sanata Ndume ya nemi afuwar jam, iyyar APC bayan ya soki gwamnatin Bola Tinubu
Idan masu bibiyar jaridar Inda ranka zasu iya tunawa dai an tsige Sanatan ne tare da maye gurbinsa da Sanata Mohammed Monguno biyo bayan wasikar da jam’iyya mai mulki ta aikewa dan majalisar na takurawa majalisar kan munanan kalamai da ya yi ba tare da kariya ko wani shakku ga shugaban kasar ba.
A cikin wasikar mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru, jam’iyyar ta umurci majalisar dattawa da ta sanyawa dan majalisar takunkumi, kasancewarsa babban jigo a jam’iyyar saboda rashin amfani da kyawawan kalamai ga jam’iyyar da Kuma zakon kasa dayakewa jam, iyyar da Kuma futo da fushin sa fila Kuma inda jam,iyyar ta zargi kuma yayi abinne da gongon
Ndume, a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, ya yi zargin cewa shugaban kasa Bola Tinubu Yana tsare a hannun sojoji a fadar shugaban kasa.
A cewar Sanatan, sojojin basa gayawa shugaban kasa gaskiya kawai Suna ciyar dashi da karya da kuma kare shi daga ‘yan Najeriya masu son kai da basa iya fadawa shugaban kasar a gaskiya.
Sukar da ya yi ta kai shi ga cire shi daga mukaminsa na babban jami’i a Majalisar Dokoki ta kasa da kuma shugaban kwamitin tsawatarwa
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
