News
Gwamnatin Kano Ta Umarci Dukkan ma’aikatan Gwamati Da Su Koma Bakin Aiki Cikin Gaggawa,
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban ma’aikatan jihar Kano, Abdullahi Musa, ya umarci dukkan ma’aikatan gwamnati da ke aiki a karkashin gwamnatin jihar Kano da su koma bakin aiki cikin gaggawa, biyo bayan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sassauta dokar hana fita daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar manema labarai da Daraktar wayar da kan jama’a a ofishin shugaban ma’aikata Bintu Nuhu Yakasai ta sanyawa hannu
Sanata Ndume Ya Nemi Afuwar Jamiyyar APC Bayan Ya Soki Shugaba Tinubu
Sanarwar ta kara da cewa Ya kuma yi kira ga dukkan ma’aikatan gwamnati da su kai rahoto ofishinsu da misalin karfe 8:00 na safe a kowace rana.
Shugaban ma’aikatan ya kuma jaddada kudirin gwamnatin jihar na inganta ma’aikatan gwamnati da inganta rayuwar ma’aikatanta.
Ya kuma jaddada bukatar kara himma wajen bunkasa ayyukan yi ga jama’a, inda ya bukaci dukkanin ma’aikatan gwamnati da su rubanya kokarinsu wajan ganin sun samu nagarta a wajan ayyukansu.
