News
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin siyar da shinkafar tallafi ga ma’aikatan Gwamnati
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnati tarayyar Nageriya ta dakatar da shirin ta na bada tallafin Shinkafa ga ma,aikatan Gwamnati don tallafamusu Kan kuɗi mai rahusa na naira duba 40 na kowanne buhun Shinkafa mai nauyin kilogiram 50 don rage radadin cire tallafin mai fetur
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wata sabuwar takardar da aka fitar daga ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati a Ranar Alhamis a Birnin Tarayyar Abuja
Sanarwar mai dauke da kwanan watan 2, Agusta , 2024, wacce Daraktan Ma’aikata na ma’aikatar, Aderonke Jaiyesimi ya sanya wa hannu Kan Kanye kudirin ta na farko akan tallafin
Har ila yau, bai nuna ko an dakatar da shirin ba kwata kwata ko kuma kawai an dakatar da shi ne
Sanarwar ta kara da cewa, “An umurce ni da in yi tsokaci kan takardar da muka yi na cikin gida a ma’aikatar (Ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatocin tarayya) na ranar 1 ga Agusta, 2024, kan batun da ke sama, in kuma sanar da ku cewa an kammala daftarin cikin gida. da nufin janyewa Kuma za,a a sanar da ƙarin cikakkun bayanai idan lokacin yayi
Tun da farko, ma’aikatar ta ce duk ma’aikatan da ke da sha’awar tsarin siyan Shinkafar zasu cika fom na Google akan yanar gizon OHCSF kuma su mika shi ga daraktan albarkatun dan adam don amincewa.
An bayyana cewa za a gudanar da biyan kudin da kuma rabon shinkafar ne ta ofisoshin da aka kebe yayin da shugaban kungiyar hadin gwiwa na ma’aikatar zai kasance mai sa ido kan wasu dalilai na gaskiya a yayin gudanar da aikin.
A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta ce ta samar da cibiyoyi a fadin kasar nan inda ‘yan Najeriya za su sayi buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan Naira dubu 40.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Muhammed Idris, ya ce shirin na daya daga cikin tsare-tsare da dama da gwamnatin Tinubu ta yi na saukaka yanayin rayuwa ga ‘ya
