News
Mun bai wa ‘yan kasuwa wa’adin wata guda su karya Farashin Kayayyakin masarufi – Hukumar FCCPC
DAGA MAHAMMAD MAHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar dake kare hakkin mai sayen kayayyaki a Najeriya ta FCCPC ta bai wa ‘yan kasuwa wa’adin wata guda a fadin kasar nan da su karya farashin kayan da suke kara masa kudi ba bisa ka’ida ba, ko kuma su gamu da fushinta.
Shugaban hukumar ta FCCPC Tunji Bello shine yayi wannan gargadin a wajen wani taron masu ruwa da tsaki a kan kasuwancin, inda ya bayyana musu shirin kaddamar da samame shaguna domin tabbatar da kawo karshen yadda ‘yan kasuwar ke kara farashin kayan masarufi ba bisa ka’ida ba.
Bello ya bada misalin yadda ake sayar da wani karamin injin din markade a Texas ta kasar Amurka a kan dala 89 ko kuma kwatankwacin naira dubu 140000, a farashin Naira amma kuma wani babban shago a Lagos ke sayar da shi a kan Naira dubu 944,0000.
Jaridar Puch ta rawaito Shugaban ya ce yadda ‘yan kasuwa ke gaban kansu wajen kara tsawwala farashin kayayyaki na yiwa tattalin arzikin kasa barazana tare da musgunawa jama’a.
Hukumar ta ce misalin bai tsaya nan ba, inda ya shafi kusan kowanne bangare ciki harda masu sayar da kayan miya da kananan kayayyakin dake shago unguwanni sabida tsadar da su Karan Kansu ababen hawa sukayi.
