Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Fara Sake Sayar Da Shaguna Da Filayen A Masallacin Idi Bayan Rushe Su Da Ta Yi A Watan Yunin Bara.

Published

on

download (2)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Gwamnatin Kano ta fara sake sayar da shaguna da filayen a Masallacin Idi bayan rushe su da ta yi a watan Yunin bara.

‘Yan kasuwa na biyan wasu amintattun jami’an gwamnatin Kano domin samun wuri (shaguna ko filaye) a wannan waje.

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Barazanar Riƙe Albashin Likitocin Da Ke Yajin Aiki A  Najeriya 

A ranar Talata ne, ɗaya daga cikin amintattun jami’an gwamnatin, Balarabe Hassan, ya yi wa ɗan jaridar PREMIUM TIMES jagoranci zuw a wajen da ke gaban masallacin Idin. A shakarar da ta gabata ne, gwamnatin jijar ta tashi ‘yan kasuwa tare da haramta musu yin kasuwanci a wannan wuri.

Malam Hassan, ya ce farashin samun wuri a filin masallacin idin ya bambanta, inda akan sayar a kan Naira 80,000 ko Naira 180,000 har zuwa Naira 1,000,000.

Advertisement

Ana kuma sayar da tebur (wurin kasa kaya da ba shago ba) a kan farashin da ya kama daga Naira 70,000 zuwa N80,000, musamman idan mai sayen yana da alaƙa mai kyau da jami’an gwamnatin.

Malam Hassan, ya kuma ce tuni wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin da amintattun ‘yan jam’iyya da aka mallaka wa wuri a masallacin suka sayar ga wasu ‘yan kasuwa.

Sannan wani ɗan kasuwa mai suna Haruna Malam, ya ce, tuni aka sanya wa teburan tambarin Hukumar Tsara Birane da Samar da Cigaba (KNUPDA), wanda hakan ke nuna akwai buƙatar mutum ya samu shaidar yin rajista daga hukumar.

Jami’an da ke ba da wannan shaidar yin rajista sun haɗa da babban mataimaki na musamman ga gwamna kan ayyukan KNUPDA, Abba Yaro, da kuma babban mataimaki na musamman ga gwamna II kan harkar Kasuwanni, Isa Wise.

Haruna Malam ya kuma ce wuraren da ke gaban masallacin idi da ke kallon titin IBB da kuma wanda ke kallon Kofar Wambai, Kasuwar ‘Yan Robobi sun fi tsada.

Wannan batu na zuwa ne bayan da gwamnatin Kano ta amince da biyan Naira biliyan 3 a matsayin diyya ga gungun ‘yan kasuwar da gwamnatin ta rushe wa shaguna a wannan wuri.

Advertisement

Gwamnatin ta biya wannan kuɗi ne a bayan fage tsakanin Kwamitin Amintattu na Mamallaka Shaguna na Masallacin Idi da kuma Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa.

An ubuta wannan ‘yarjejeniya ce a ranar 12 ga watan Disambar shekarar bara a gaban Alƙalin Babbar Kotun Tarayya, Inyang Ekwo, da ke Abuja bayan shigar da ƙara da masu shagunan suka shigar da gwamnatin Kano da KNUPDa da Babban Jojin Kano.

Sauran waɗnda aka yi ƙara sun haɗa da: Mataimakin Sufeto-janar na ‘yan sanda na shiyya ta ɗaya a nan Kano da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano da Kwamandan Rundunar Kare Al’umma da Kadarorin Gwamnati (NSCDC) na Kano da na ƙasa.

Wannan mataki na kai ƙara ya biyo bayan da gwamnatin Kano ta rushe shagunan tare da cewa gwamnatin da ta gabace ta ta sayar da shagunan da aka gina a filin masallacin idin ne ba bisa ƙa’ida ba ga ‘yan kasuwar.

Sai dai bayan biyan ‘yan kasuwar diyya, gwamnatin ta dawo tana sake sayar da wannan wuri ga wasu ‘yan kasuwar.

Daraktan Gudanarwa na Hukumar KNUPDA, Ibrahim Adamu da kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Baba Halilu Dantiye, ba su ce komai ba kan wannan al’amari duk da kira da saƙon kar ta kwana da aka aike musu kan wannan batun.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending