News
YANZU-YANZU: Kano Ta Sanar Da Sabuwar Ranar Da Za A Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta sanya ranar gudanar da zaben kananan hukumomi nan da wata guda.
Shugaban Hukumar KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya sanar da sauya ranar a wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
Rahotanni na nuni da cewa da farko, hukumar ta tsara zaɓe a ranar 30 ga Nuwamba, duk da haka, za a gudanar da zaɓe a ranar 26 ga Oktoba, 2024.
Ya ce an yanke shawarar gajarta lokacin zaɓen ne don yin biyayya ga hukuncin Kotun Koli da ta bai wa ƙananan hukumomi yancin cin gashin kansu.
Advertisements
