News
Ƴan Bindiga sun kashe Diliban Makaranta a jihar Yobe
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe dalibai a makarantar Faudiya mallakin ‘yan Shi’a da ke karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe.
Jaridar Daily Trust ta rawaito Harin mayakan Boko Haram ya rutsa da Daliban Makarantar Faudiya dake karkashin kungiyar Musulunci ta Shia,a ne a Ranar Juma,a da misalin Karfe 3:44 na Asuba.
Jaridar ta,ce Mayakan Boko Haram tunda fari sun mamaye Unguwar Hausari da ke karamar hukumar Geidam domin shirin su na kai harin cikin makarantar.
Yan Bindingar sunkai harin daidai lokacin da daliban ke tsaka da barci.
Rahotanni sunce mayakan sun kai hari makarantar ne a lokacin da wadannan matasan ke tsaka da barci suka kuma fito da su waje suka harbe su har lahira.
Tun bayan faruwar lamarin ne Kuma Al, umma suka shiga tashin hankali da damuwa da fargana a garin bayan a cewar majiyar.
Wasu Yan Banga sun bayyana cewa an kashe ‘yan kungiyar Shi’a uku yayin da Daya daga ciki ya samu mummunan rauni.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ki bayar da cikakken bayani.
