Connect with us

News

Kungiyar SERAP Ta Kai Karar  Shugaban Majalisar Dattawa Da Kakakin Majalisar Wakilai Kotu

Published

on

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci a Nijeriya

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci a Najeriya ta maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas gaban kotu kan kawo karshen kayyade alawus-alawus dinsu.

Rahotanni na nuni da cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi zargin cewa ‘yan majalisar su ke yanke na kansu albashi da alawus-alawus.

Advertisement

Sai dai Majalisar ta musanta wannan zargi.

A cikin karar da aka shigar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1289/2024 a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman da a tilasta wa Akpabio da Abbas su kawo karshen wannan lamari na kayyade albashi da alawus-alawus.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending