Connect with us

News

Hanyoyin Samun Shinkafar Gwamnatin Tarayya Mai Rahusa 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnatin tarayya ta ce ma’aikatan gwamnati waɗanda suke da lambar ɗan ƙasa ta NIN ne za a bai wa damar sayen shinkafar da gwamnatin za ta sayar a farashi mai rahusa.

Advertisement

Ministan Noma, Abubakar Kyari ne ya sanar da hakan, inda ya ce hakan zai taimaka wajen rage ci da zuci da kuma saye abincin a kasuwa da ma rage tsadar abincin a kasuwannin Najeriya.

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Amince Da Ƙudirin Ƙirƙiro Hukumar Inganta Karatun Tsangaya

Abubakar Kyari ya ce a ƙarƙashin tsarin, “buhu ɗaya kawai mutum zai samu.”

Advertisement

Ya ce buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 za a sayar a farashin Naira 40,000 a cikin shirin gwamnatin na rage raɗaɗin tsadar kayan masarufi.

Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa  ministan na cewa sai wanda ya mallaki shaidar ɗan ƙasa wato NIN ne kawai zai samu damar sayen shinkafar.

Advertisement

Ya ce an saki tan 42,000 na kayan masarufi, da kuma tan 30,000 na shinkafa wanda za a sayar wa ƴan Najeriya.

Ya ce ana sa ran fitar da abincin na gwamnati zai sa farashin abincin ya sauka a kasuwanni.

Advertisement

Darakta, ɓangaren abinci da tsare-tsaren tanadi na ma’aikatar, Haruna Sule Abutu ya bayyana sharaɗin da za a cika domin samun damar sayan abincin kamar haka:

Dole mutum ya mallaki lambar ɗan ƙasa ta NIN

Advertisement

Lambar waya

Rajista da IPPIS idan ma’aikacin gwamnati ne

Advertisement

Ya ce idan mutum ya zo wurin sayar da shinkafar da abubuwa guda uku, za a tantance shi, sai a ba shi wata lamba da rasitin da mutum zai kai wajen da ake karɓa ya ɗauko shinkafarsa.

Ya ƙara da cewa a jikin rasit ɗin kowa akwai lokaci da wajen da zai je ya ɗauki tasa shinkafar.

Advertisement

 

PRNIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending