News
Kowa Na Da Damar Sayen Mai A Matatar Dangote — Kamfanin NNPC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kamfanin mai na Najeriya, NNPC ya musanta zargin da ya ce ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya, MURIC ta yi masa na yi wa matatar mai ta Dangote maƙarƙashiya.
Kungiyar MURIC ta yi zargin cewa ƙarin kuɗin mai da NNPC ya sanar a baya-bayan nan zai hana matatar Dangoten sayar da man a farashi mai rahusa, sannan ta yi zargin cewa kamfanin NNPC ne kawai zai riƙa sayen mai daga matatar.
DA DUMI-DUMI: Ajuri Ngelale Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Yada Labarai Ya Yi Murabus
To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Asabar, ya musanta zargin, yana mai cewa kasuwa ce ke ƙayyade farashin man kowace matata ciki kuwa har da ta Dangote.
”Ƙarin kuɗin mai da aka samu a baya-bayan nan ba zai hana matatar Dangote ko duk wata matata a cikin ƙasar nan samun ciniki ba. Idan ma suna ganin kamar kuɗin ya yi yawa, to matatar ta samu damar da za ta rage farashi domin samun ciniki a kasuwa”, in ji sanarwar.
Haka kuma NNPCL ɗin ya ce babu tabbacin samun ragin rafashi kan man da aka tace a gida fiye da yadda ake sayar da shi a kasuwar duniya, kamar yadda matatar Dangoten ta tabbatar masa.
Kamfanin NNPC, ya ƙara da cewa zai sayi man Dangote ne kawai idan farashin man a kasuwar duniya ya fi yadda ake sayar da shi a Najeriya, don haka matatar Dangote da sauran matatun cikin gida na da damar sayar da man ga duk wanda ke buƙata a kan farashin da suka daidaita.
”NNPC ba shi da niyyar kankane sayar da man shi kaɗai a fagen kasuwancin da kowa ke da damar shiga a dama da shi, don haka maganar a ce NNPC ne zai sayi mai daga matatar ba ta taso ba,” in ji sanarwa.
Kamfanin ya kuma ce babu ta yadda zai yi maƙarƙashiya ga kasuwancin da ya zuba hannun jarin biliyoyin daloli a cikinsa.
-
News2 days agoWani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
