News
DA DUMI-DUMI: Ajuri Ngelale Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Yada Labarai Ya Yi Murabus
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ajuri Ngelale, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, zai dauki hutun da ba zai wuce iyaka ba, domin mayar da hankali kan harkokin kiwon lafiya na kashin kansa.
Ajuri Ngelale ya ce, “A ranar Juma’a, na mika takarda ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, inda na sanar da ofishina cewa zan tafi hutun da ba a iya tantancewa ba don tunkarar al’amuran kiwon lafiya da suka shafi dangina
Za Mu Haskawa Matasa Damammaki A Ɓangaren Harkar Ƙera Ababen-hawa A Najeriya —Hukumar NADDC
“Yayin da nake matukar godiya da cewa jirgin kasa ba ya jiran kowa, wannan yanke shawara mai ban tausayi wanda ya haifar da dakatar da ayyuka na a matsayin mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai . Inji Ajuri Ngelale
Na zartar da wannan muhimmin shawarar ne bayan tattaunawa da iyalina. Ina fatan kowa zai mun afuwa bisa kuskure na ɗan adam da ake samu a wasu lokuta Nagode.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News4 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News6 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
