Connect with us

News

Za Mu  Haskawa Matasa Damammaki A Ɓangaren Harkar Ƙera Ababen-hawa A Najeriya —Hukumar NADDC

Published

on

IMG 20240907 WA0009

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Za Mu  Haskawa Matasa Damammaki A Ɓangaren Harkar Ƙera Ababen-hawa A Najeriya

 

Advertisement

—Hukumar NADDC

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar Kula da Ƙere-ƙere da Samar da Ababen-hawa ta Ƙasa, NADDC, da hadin gwiwa da Ofishin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Cigaban Matasa, Sanya Ido da Aiwatar da ayyuka, na daf da yin wani gangamin taro na bajekolin fasaha da nufin haskawa matasa damammaki a ɓangaren ababen-hawa da sufuri a Najeriya.

Advertisement

Taron, wanda za a gudanar a ranar 11 da 12 ga watan Satumba a Musa Yar’Adua Centre in Abuja, zai haska damammaki a ɓangaren sabuwar fasahar amfani da iskar gas a ababen-hawa, CNG, amfaninda wajen bunkasa tattalin arziki da kuma amfanin sa da tsari da yake da shi a ababen-hawa.

An Kashe Mutane 13,346 Da Sace 9,207 Daga Zuwan Shugaba Tinubu  – Rahoto

Mr. Rosilu Emmanuel, Mataimaki na Musamman kan dabarun aiki ga shugaban, NADDC, Mr. Oluwemimo Joseph, a wata sanarwa da ya fitar ya ce taron zai nunawa matasa hanyoyin samun arziki a bangaren ababen-hawa da sufuri.

Advertisement

Ya kara da cewa a taron, NADDC za ta ƙaddamar da gasar zanen ƙera mota mai amfani da iskar gas domin baiwa matasa damar bajekolin fasahar su da kuma karfafa musu gwiwa a fannin.

Ya kara da cewa “masu sha’awar shiga gasar za su aiko da faifain bidiyo na mintinan 2 zuwa 3 su nuna irin fasahar su a ciki zuwa addressing imel na naddcouncil@gmail.com daga ranar 1 zuwa 9 ga watan Satumba.”

Advertisement

Ya kara da cewa masana da masu ruwa da tsaki a harkar ƙere-ƙeren ababen-hawa da sufuri ne za su halarci taron.

Ya kara da cewa; Manyan baki da za su halarci taron sun hada da Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Hon. (Dr.) Doris Uzoka-Anite, Ministan Kasuwanci da Masana’antu, Shugaban hukumar NADDC, Mr. Oluwemimo Joseph Osanipin, Mataimakin Shugaban ƙasa kan harkokin matasa, Hon. Titilope Gbadamosi, inda hakan zai kara wa matasa kaimi wajen cika burin su a fannin,” in ji sanarwar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending