Connect with us

News

An Kashe Mutane 13,346 Da Sace 9,207 Daga Zuwan Shugaba Tinubu  – Rahoto

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Alkaluman mutanen da aka kashe a Najeriya tun bayan rantsar da shugaba Bola Ahmad Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun shakarar 2023, ya kai dubu 13,346 yayin da aka yi garkuwa da mutun 9,207 a sassan Najeriya.

Rahoton wanda wata cibiyar tsaro ta Beacon Consulting, ta fitar ya nuna cewa al’amuran rashin tsaro da kashe-kashe sun yi ƙamari a cikin wannan shekara, inda aka kashe mutane dubu 7,544 tare da garkuwa da mutum dubu 6,453 tsakanin watan Janairu zuwa Satumba.

An Kashe Mutane 13,346 Da Sace 9,207 Daga Zuwan Shugaba Tinubu  – Rahoto

Rahoton cibiyar ya nuna yadda aka samu ƙaruwar tashe tashen hankulan da ya shafi kananan hukumomi 667 na ƙasar, wanda ta alakanta su da ta’addanci da ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane da rikicin manoma da makiyaya, da dai sauran nau’ikan tada zaune tsaye.

Masana dai na nuna damuwarsu kan kalubalen tsaro da ke kara ta’azzara, sun kuma yi kira ga shugaba Tinubu da ya dauki kwararan matakai.

Haka Na Gaji Matsalar Tsaro – Shugaba Tinubu

Advertisement

A wani taron tsaro da zaman lafiya da ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma suka shirya a jihar Katsina a watan Yuli, Shugaba Tinubu ya bayyana rashin tsaro da ake fama da shi musamman a yankin Arewa maso Yamma a matsayin wanda ya gada daga gwamnatotin baya.

 

FRI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending