News
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga A Borno, Filato Da Kaduna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga sannan sun kama wani mai safarar makamai dake da alaka da wani mashahurin dan bindiga da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo.
A ranar 3 ga Satumba dakarun dake samar da tsaro a karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno sun afka wa ƴan bindiga dake tsaunukan Mandara. Dakarun sun ceto mutum 24 da maharan suka yi garkuwa da su bayan nasara da suk yi a kansu.
Man Fetur Din Dangote Zai Fara Isa Kasuwa Makon Gobe – Kamfanin NNPC
Sojojin sun kwato bindigogi da harsasai ma su yawa.
Daga nan a jihar Kaduna kuma dakarun sun kashe wani hatsabibin dan bindiga a kauyen Kabode dake karamar hukumar Kachia sai dai sauran ƴan bindigan sun gudu.
Dakarun sun ceto mutum hudu da maharan suka yi garkuwa da su sannan sun kwato AK-47 daya, harsasai 10, babura shida da wayoyin hannu uku.
“Dakarun tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai hari tsaunin Keyeri da Gidan Dogo dake karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna inda suka kama wani dake safarar makamai wa mahara a dakin Gidan Dogo.
“Dakarun sun kwato bindiga kirar AK-47 uku, bindiga kirar Galil daya da harsasai da dama.
“Binciken da jami’an tsaron suka gudanar kan mai safarar muggan makaman ya taimaka wajen kama wasu masu safarar makamai 8.
Bayan haka dakarun dake samar da tsaro a jihar Filato sun kai farmaki a maboyar mahara a karamar hukumar Riyom inda har suka kama ‘yan bindiga biyu sannan sun kwati wayoyin hannu biyu da wuka.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
