Connect with us

News

Buncike Ya Gano Rashin Kwarewa Ne Ya Tilastawa Ajuri Ngilale Yin Murabis Daga Mukaminsa

Published

on

IMG 20240907 WA0023

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

A Safiyar jiya Asabar ne Kakakin shugaba Bola Tinubu, Ajuri Ngelale ya mika takardar ajiye aiki wanda a cikin wasikar ya ce zai je ne don ya kula da iyalansa da basu lafiya kuma suna buƙatar sa kusa.

Sai dai kuma a wani buncike da Jaridar PREMIUM TIMES tayi ta binciko ta da gano ainihin abinda ya sa Ngelale ya ajiye aikinsa.
Bunciken ya ce ya gano cewa an kwana biyu ana zaman doya da manja tsakanin ofishin shugaban kasa da Ngelale saboda abinda suka ce ba shi da kwarewar da ake so wanda zai rike wannan muƙami.

Advertisement

Tun farko ma dai ɗan shugaba Tinubu ne Seyi Tinubu ya bada sunansa a yi masa kakakin shugaban kasa, amma kuma kwarewarsa, da sanin faɗi tashin aikin jaridarsa ya yi ƙaranci matuƙa ace wai shine ke magana da yawun shugaban kasa.

A bincike da jarida ta yi ta gano ba shi da gogewa kan aikin da ya ke yi, bai goge wajen iya mu’amula da mutane ba da kuma manyan jami’ai musamman ta harkar kare ofishin shugaban kasa da tattare bayanai da watsa su yadda ya kamata.

Advertisement

” Da farko dai, kwarewarsa a harkar jarida, ya yi karanci matuka, sannan kuma ba a cikin Najeriya ba, bai da wata alaka da gogewa kan lamuran kasashen duniya da kuma abokan aiki da suka kware a ciki da wajen Najeriya.

Ngelale, baya ga ƙarancin shekaru, da rashin sanin yadda ya kamata a rika tunkarar aikin magana daga ofishin shugaban kasa, duk da haka ya rika nuna zai iya aikin.

Advertisement

Sai dai kash, daga baya-bayan nan abin nasa sai ya rika taɓarɓarewa, ya sa dole fadar ta nemo wani da ya ke da kwarewa a harkar domin ya rike wannan muƙami na kakakin shugaban kasa.

An ba shi damar ya sauka daga kujerar, a nada wani don su rika aiki tare yana ƙarƙashinsa amma ya nuna nan ɗin dai yake so.

Advertisement

Hakan yasa, dole ya ajiye aikin domin a baiwa wani kwararre a fannin

Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin nasa.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending