News
Wani Saurayi Ya Zuba Wa Budurwarsa Fetur Sannan Ya Cinna Ma Ta Wuta Saboda Ta Yanke Alaƙarsu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata yarinya tana cikin halin ha’ula’i bayan da saurayinta ya cinna mata wuta saboda ta yanke alaƙarsu.
Yarinyar ’yar shekaru 13 ta gamu da ƙuna har kusan kashi 90 na jikinta bayan tsohon saurayin na ta mai shekaru 19 ya zuba ma ta fetur sannan ya cinna ma ta wuta.
Rushewar Gine-Gine Ta Yi Sanadiyar Rasuwar Mutane Fiye Da 90 A Shekara Daya A Najeriya
Wilson Jaɓier Melendez Bonilla, mai shekaru 19, ya shiga gidan yarinyar ne da ke kudu maso yammacin garin Cabo Rojo na ƙasar Puerto Rican, a daren ranar asabar ya same ta tana barci a kan shimfiɗa, sannan ya watsa ma ta fetur a jiki ya banka mata wuta a wani abin da aka bayyana a matsayin laifin son rai.
Mahaifiyar wacce aka kashe, Nanette Camacho, ’yar shekaru 34, ta samu ƙananan raunuka a fuskarta da hannayenta lokacin da take ƙoƙarin ceto ‘yarta. ƙanin yarinyar mai shekaru tara shima ya ƙone yayin harin, amma raunin da ya samu ba na barazanar rai bane.
Da farko an kai yarinyar asibiti a lokacin da likitoci suka yi ma ta allurar kashe zafi, sannan suka mayar da ita zuwa wani asibiti.
Bonilla, wanda ya kasance a gida lokacin da ’yan sanda suka zo don kama shi, an tuhume shi da laifuka bakwai, ciki har da zargin kisan kai uku.
BLUEPRINT
