Connect with us

News

Yan Sandan Kano 5 Sun Rasu Sanadiyyar Hatsarin Mota A Hanyarsu Ta Dawowa Edo

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Yan sandan Kano 5 sun rasu Sanadiyyar hatsarin mota a hanyarsu ta dawowa daga jihar Edo, inda suka je don aiki na musamman yayin gudanar da zaben Gwamnan jihar da aka gudanar a Ranar Asabar .

Freedom Radiyo ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a daren jiya, a garin Karfi dake  Karamar Hukumar Kura da ke Kano.

Rahotanni na nuni da cewa motar yan sandan ta kamfanin Kano Line ta yi karo da babbar motar Tirela.

Bayanan sirri daga majiyar Freedom Radiyo  na nuni da cewa Yan sandan da suka rasu sun hada da Insfecta Usman Salishu da Sajan Umar Muhammad da Kofur Kamalu Shehu sai kuma Sajan Sa’idu Salisu da Kofur Abubakar Nuhu da suka rasu bayan an garzaya da su Asibiti.

Baya ga wannan Yan sanda goma ne suka jikkata wadanda yanzu haka suke samun kulawa a Asibitin Kwararru na Murtala.

Advertisement

Game da wannan hatsari mun tuntubi Kakakin Yan sandan Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa amma ya ce zai bincika.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending