Connect with us

News

Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Fara Ɗaukar Salon Mulkin ‘Kama-Karya’ — Premium Times

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Biri da gatari kashe mai gona. Kamar haka ‘yan Najeriya suka fara gani daga makonni kaɗan da suka gabata, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta fara fitowa ƙarara ta nuna siffofi da sagwangwaman gaba da kuma ƙiyayya ga dimokraɗiyya.

Advertisement

Hakan ya fara cusa damuwa a zukatan jama’a dangane da alƙiblar da mulkin Tinubu ya fuskanta, a cikin watanni 16 bayan hawan sa mulki.

Yan Sandan Kano 5 Sun Rasu Sanadiyyar Hatsarin Mota A Hanyarsu Ta Dawowa Edo

Dimokraɗiyyar da mulkin Fir’aunanci dai duk mun sani cewa ba su taɓa zama inuwa ɗaya.

Advertisement

Kuma ba zai yiwu a ce a hautsina su biyun wuri ɗaya ko tare da juna ana gudanar da su ba.

Makonni biyu baya, ‘yan Najeriya sun tashi da mamaki da al’ajabin yadda jami’an DSS suka yi ƙumumuwar afkawa ofishin ƙungiyar kashe dimokraɗiyya da sa-ido kan samar da nagartacciyar gwamnati, wato SERAP, wai sun je su na neman daraktocin ƙungiyar.

Advertisement

Wannan kuma ko ta wace fuska za a kalli lamarin, karan-tsaye ne aka yi wa dimokraɗiyya.

Afka wa ofishin Kungiyar SERAP a Abuja da aka yi, ya faru kwanaki kaɗan bayan ƙungiyar ta la’anci yadda kamfanin NNPCL ya ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya, ta yadda ba a yi aune ba, sai ya ƙara farashin litar fetur, ba tare da shawara ko tuntuɓa ko sanarwa ba.

Advertisement

Daga 1999 zuwa wannan shekara an yi gadangarƙama da ƙaƙudubar dagargaje Dala biliyan 25 wajen yi wa matatun man Najeriya huɗu garambawul da gyare-gyare, amma har yau fetur cikin ledar ‘pure water’ ɗaya ba su iya tacewa.

Ba su tsinana komai ba sai gurgunta kasuwanci, karya ‘yan kasuwa, dakushe hada-hada, ƙara tsadar kuɗaɗen motocin haya, yadda har talaka ya gwammace ya yi tafiya a ƙasa maimakon tatuke kuɗin abincin da na iyalin sa ya shiga mota da su.

Advertisement

Tsadar fetur ta haifar da tilas ma’aikatan gwamnati sun daina zuwa ofishin a kowace rana. Wasu ma sau ɗaya ko sau biyu su ke zuwa ofis a kowane sati.

An ƙirƙiro mafi muni kuma mafi illar maƙarƙashiya da zagon-ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa da na al’ummar cikin ta.

Advertisement

SERAP ta yi kira ga gwamnatin Tinubu ta janye ƙarin fetur daga Naira 855 ta maida shi Naira 600. Ana tsakiyar haka kuma dai SSS suka kama Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Joe Ajaero, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, a ranar 9 ga Satumba. Kafin sannan dama an tsare Ajaero bisa zargin sa wai da ɗaukar nauyin ta’addanci. Wannan kuma aikin kamen ‘yan sanda suka yi shi. Sun yi gaggawar sakin sa bayan sun ga ɗaukacin ma’aikatan faɗin ƙasar nan sun yi barazanar tafiya yajin aiki, idan aka ƙara sa’o’i 24 ba su sake shi ba.

An kama shi ne biyo bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a faɗin ƙasar nan ta tsawon kwanaki 10.

Advertisement

Sai kuma gugumarar sabon farashin fetur, bayan NNPCL ta fara sayen fetur a Matatar Ɗangote, wanda a yanzu lita ɗaya ta kai N1,029 a Jihar Barno.

Bulalar mulkin Fir’aunancin da Gwamnatin Tinubu ke tsala wa ‘yan Najeriya, ba ta ƙyale ‘yan jarida ba. Cikin watan Fabrairu, an damƙe sojoji sun kama babban mai rahoton Galaxy TV a Warri, suka garƙama masa ankwa. Saura irin su Madu Onuorah, Daniel Ojukwu, Dayo Aiyetan, Nuruddeen Akwasika da Adejuwon Soyinka duk sun ɗanɗana zafin bulalar mulkin Fir’aunancin gwamnatin Tinubu.

Advertisement

Shi kuwa wakilin PREMIUM TIMES, Abdulkarim Mojeed, shi da abokan aikin sa uku, Allah ne dai ya sa su na da tsawon rai. Domin ‘yan sanda ne suka buɗe wa motar su ruwan harsasai suka ratattake ta, lokacin da suke ɗaukar rahotanni wurin zanga-zangar tsadar rayuwa cikin watan Agusta, a Babban Filin Wasa na Abuja.

Duk wanda ya yi harbi kan waɗanda ba su riƙe da makamai, ya yi ne da nufin kisa kawai. Wannan kuma ba dimokraɗiyya ba ne. Biri ne da gatari a cikin gonar mai gona. Ba noma ya je taya shi ba, kashe shi ya je ya yi.

Advertisement

Ya kamata gwamnatin Tinubu ta sani cewa duk wani duk wani yunƙurin daƙile masu rajin kare dimokraɗiyya ko maƙure kafafen yaɗa labarai da ‘yan jarida, to ba zai yiwu ba a ƙasar nan. Duk mai wannan mafarkin ma ya farka. Domin tuni dokar ƙasa ta bayar da ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma ‘yancin ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai, a Sashe na 39 (1) da na 40 a Kundin Dokokin 1999.

Shi kan sa Tinubu tsohon ɗan gwagwarmaya ne, ya fi kowa sanin ciwon dankwafe haƙƙi da ‘yancin faɗar albarkacin baki. Su ne manyan jiga-jigan yi wa gwamnatin Goodluck Jonathan zanga-zangar yunƙurin ƙarin kuɗin fetur a 2012. Kuma tsohon gogarman ɗan NADECO ne, a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha. An taɓa tuhumar sa da cin amanar ƙasa cikin 1994, ya arce ya bar ƙasar.

Advertisement

PREMIUM TIMES ta yi tir dangane da yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin maida duk wanda ya nemi ɗaga murya zuwa fursunan siyasa. A daina wannan Fir’aunancin.

Bai yiwuwa a ce a rufe bakin masu ‘yancin faɗin albarkacin bakin su, a daidai lokacin da gwamnati ba ta jin kunya ko tausayin talakawa wajen dagargazar kuɗaɗe da taɓargaza da ɓarusa. Shi kuwa talaka an bar shi cikin masifar ƙuncin rayuwa, raɗaɗin tsadar kayan abinci da tarangahumar tsadar fetur. Ai kuwa da sakyel, wai an dafa kaza, an raba, an ba mai kaza kan kazar kaɗai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending