Connect with us

News

Majalisar Kogi Ta Bukaci Shugaba Tinubu Ya Gaggauta Tsige Shugaban Hukumar EFCC

Published

on

1727192124022

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

 

Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta nemi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, wanda ta zarga da kawo ruɗani a batun binciken tsohon gwamnan jihar, Kogi Yahaya Bello.

Advertisement

Majalisar ta zargi hukumar dayin  shisshigin kutsawa Gidan Gwamnatin Kogi da ke Abuja, wanda EFCC suka yi harbi a cikin gidan.

Jaridar Puch ta rawaito EFCC ta afka cikin Gidan Saukar Baƙi na Gwamnatin Kogi a Abuja cikin makon jiya, domin kamo Yahaya Bello, wanda Hukumar tayi zargin cewa yana cikin gidan.

To sai dai ‘yan majalisar sun ce EFCC ta keta doka da ta yi harbi a cikin gidan, gwamnati kuma hakan da suka yi, yunƙuri ne na kashe Gwamnan Kogi da ke kan mulki a yanzu haka wato Gwamna Ahmed Ododo.

Kakakin Majalisar Kogi, Aliyu Yusuf, ya ce “abin da EFCC ta yi ya nuna irin yadda hukumar ba ta girmama tafarkin dokokin ƙasa, ta saka siyasa a batun yaƙi da cin hanci da rashawa.

A zaman ta ranar Litinin, majalisar ta yi kira ga Shugaba Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar EFCC, Olukoyede, “saboda bai ƙware wajen yaƙi da cin hanci da rashawa ba, ya saka siyasa a cikin aikinsa.”

Majalisar ta ce abin da EFCC ta yi a Gidan Gwamnatin Jihar Kogi a Abuja, zai iya lahanta Gwamna Ododo da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.

Advertisement

‘Yan Majalisa irin su Akus Lawal, Jacob Olawunmi da kuma Abu Jibril mai wakiltar ƙaramar hukumar Ajaokuta, duk sun nemi a gaggauta gurfanar da Shugaban EFCC Kuma a hukunta shi.

Jibril ya ce Shugaban EFCC da kan sa ya umarci jami’an sa su yi harbi a cikin Gidan Gwamnatin Jihar Kogi a Abuja, inda tsohon gwamnan ya nemi mafaka

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da aketa samun sabanin bayanai na cewa tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahya Bello ya’kai kansa ga hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa inda Hukumar ta musunta cewar tsohon Gwamnan baya hannunta.

 

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending