News
Zan Cigaba Da Bayar Da Goyon Baya Wajen Kawar Da Cutar Shan Inna A Karamar Hukumar Tarauni —Shugaban Riko
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban riko na Karamar Hukumar Tarauni kuma Daraktan Mulki da kudi Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu yabada tabbacin cigaba da bayar da goyon baya wajen kawar da cutar shan inna a yankin.
Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu ya ba da wannan tabbacin ne a yayin taron kwamitin kartakwana na rigakafin cutar shannina da aka gudanar a ofishinsa dake sakariyar karamar hukumar Tarauni.
Kotu Ta Dakatar Da Jam’iyyu 21 Hana hukumar KANSIEC Karbar Kudaden Fom Din Tsayawa Takara.
Alh Abdulkadir Muhammad Arabu Ya jaddada kudirin karamar hukumar na kawar da cutar shanninah gaba daya tare da tabbatar da cewa dukkan yara a yankin sun samu rigakafin da ya kamata a wannan zagayen da za a gudanar na rigakafin.
A yayin taron, kwamitin ya duba nasarorin da aka samu zuwa yanzu tare da tsara dabarun shawo kan kalubalen da aka fuskanta yayin yakin rigakafin Daya gabatar
Shugaban rikon karamar hukumar Alh Abdulkadir Muhammad Arabu ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da ma’aikatan lafiya da shugabannin al’umma, da su kasance masu himma da hadin kai wajen ganin an samu yankin da babu Mai dauke da cutar shan inna.
Jami’ar kulada lafiya a matakin farko ta karamar hukumar Tarauni Hajiya Saratu Ibrahim ta yi kira ga iyaye yara da masu dasu tabbatar da an yi wa yaran su ‘yan kasa da shekara biyar rigakafin za a gudanar a ranar Asabar Mai zuwa.
Hajiya Saratu Ibrahim Ta Kara da cewa rigakafin shi ne hanya mafi inganci ta kare lafiyar yaran tare da kiyaye su daga illar cutar shan inna.
Daganan Hajiya Saratu ta jaddada cewa karamar tace hukumar ta himmatu wajen yakar cutar shan inna a yankin baki daya, kuma za ta ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace don kawar da cutar daga yankin.
A nasa jawabin, Hakimin Tarauni (Dan Goriban Kano), Alhaji Ado Kurawa ya tabbatar da ci gaba da wayar da kan al’ummar yankin kan muhimmancin yin rigakafin shan inna ga yara ‘yan kasa da shekara biyar.
A jawabin sa Jami’in ilimantarwa aKan harkokin lafiya na yankin, Mallam Musa Abdullahi shamakawa ya yaba wa Hakimin Tarauni Dan Goriban Kano Alh Ado kurawa, dagatai da masu Unguwanni, dakuma Limamai bisa kokarinsu na wayar da kan Alumma akoda yaushe kan rigakafin cutar shan inna a yankin.
