Connect with us

News

Tsadar Wake Na Ci Gaba Da Karya Jarin Masu Sana’ar Kosai A Kano

Published

on

Tsadar Wake Na Ci Gaba Da Karya Jarin Masu Sana'ar Kosai A Kano

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Mafi akasarin masu sana’ar sayar Kosai a cikin birnin Kano sun daina kasuwanci saboda tsadar wake da man girki a jihar .

Advertisement

Kosai, wanda aka fi sani da Akara a wasu sassan Najeriya, Abinci ne da aka fi amfani da shi don karin kumallo a yankuna da dama na Arewacin Najeriya ciki har da jihar Kano.

Duk Inda Kuka Ga Abincin Bati Kawai Ku Ci — Akpabio Ya Gargadi ‘Yan Najeriya

Tsadar kayan masarufi ya wuce gona da iri a ‘yan kwanakin nan, domin galibin masu yin sana’ar jihar ba za su iya cigaba ba sakamakon tsadar wake da man gyada yayi.

Advertisement

A yanzu dai ana sayar da wake tsakanin Naira 3,800 zuwa Naira 4,200, gwargwadon irin nau’in da ake samu a kasuwa, yayin da man gyada da aka fi soya ƙosan, ana sayar da shi tsakanin Naira 1,700 zuwa Naira 1,900.

Wani bincike da jaridar PRIME TIMES ta gudanar a sassan birnin Kano da suka haɗa da Kurmawa, Indabawa, Mubi, Tarauni da Nasarawa, ya nuna cewa galibin masu sayar da ƙosan sana’ar ta gagare su a halin yanzu.

Advertisement

Wasu kuma sun koma Gurasa, abincin gida da ake yi da fulawa, da sukari, ko kuma wainar wake.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending