News
Wani Bene Mai Hawa 2 Ya Ruguje A Legas
Advertisements
Advertisements
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani bene mai hawa 2 ya ruguje a kan titin Amusu, dake shiyar Orile Iganmu ta jihar Legas.
Bene ya ruguje ne da safiyar yau Litinin a yayin da mutane ke shirye-shiryen fara gudanar da harkokinsu.
Wata Babbar Mota Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mata Da Miji Akan Hanyar Sagamu-Ogijo
Wani mamallakin jaridar intanet, Samuel Olatunji, ya wallafa bidiyon ginin lokacin da yake rushewa, a shafinsa na Instagram.
Ba a iya tantance adadin mutanen dake cikin ginin lokcin da ya rushe ba.
Sai dai, sanarwar da tawagar daukin gaggawa ta hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta fitar tace, rushewar ginin bai rutsa da kowa ba
Advertisements
