Connect with us

News

Makarantun Gwamnati A Sabon Gari Sun Zama Maboyar Masu Aikata Laifuka —Bincike

Published

on

Makarantun Gwamnati A Sabon Gari Sun Zama Maboyar Masu Aikata LaifukaBincike

DAGA SALISU BASO

Wani bincike da aka gudanar na nuni da cewa an kwace makarantun gwamnati guda uku a yankin Sabon Gari, inda Makarantun suka zama maboyar ‘yan fashi da makami.

Advertisement

Makarantun da ake magana a kai su ne Maikwatashi Secondary School, Zawa’i Junior Secondary School, and Government Girls Secondary School Maikwatashi, duk suna kan titin Igbo a unguwar Sabon Gari.

Fubara Ya Amince Da Biyan Mafi Karancin Albashi Na N85,000 Ga Ma’aikatan Jihar.

Waɗannan Makarantun An mamaye Waɗannan makarantun masu aikata laifuka dauke da muggan makamai sun mamaye yankin, hakan na barazana ga lafiyar dalibai da ma’aikata, da kuma kawo cikas ga yanayin karatun daliban.

Advertisement

Lamarin ya sa iyaye da masu kula da yara da dama suka janye ‘ya’yansu, daga zuwa makaranta saboda wannan lamarin.

Yanzu haka dai dalibai hudu ne kawai ke zuwa makarantar Zawa’i Junior Secondary School saboda makarantun sun zama maboyar miyagu da ‘yan daba.

Advertisement

Haka zalika Makarantun sun lalace gaba daya, ba rufi,ba tagogi, ko kofa, su kansu gine-ginen sun tsattsage ga matsalar tsaro.

Da aka tuntubi hukumomin makarantar da Kano State Senior Secondary Schools Management Board (KSSSMB) da kungiyar iyaye da malamai ta (PTA) sun bayyana cewa an aika wasiku da dama ga hukumomin da abin ya shafa kan harkokin tsaro da samar da ababen more rayuwa da suka shafi makarantun.

Advertisement

Mista Samuel Mbadwe, mamba a kwamitin kula da makarantu (SBMC) a GSS Maikwatashi, ya nuna damuwarsa kan halin da makarantar ke ciki da rashin tsaro.

Ya bayyana cewa kwamitin SBMC ya yi iya bakin kokarinsa wajen shiga tsakani amma bai samu nasara ba saboda kalubalen tsaro da ake fuskanta.

Advertisement

Lamarin dai ya ja hankalin majalisar dokokin jihar inda ta umarci kwamitin ta na ilimi da ya binciki kudirin da Hon. Yusuf Bello Aliyu, mamba mai wakiltar mazabar Nassarawa ya yi.

Kudirin ya bukaci a mayar da makarantun zuwa unguwar Kaura Goje, saboda yawancin daliban sun fito ne daga makwabtan yankunan kamar Brigade, Tudun Wada, da Gwagwarwa.

Advertisement

A cikin ajujuwa goma, uku ne kawai ake amfani da su a halin yanzu, yayin da masu laifi da ‘yan daba suka mamaye sauran filin.

Kwamitin ya ba da shawarar cewa gwamnati ta magance wadannan matsaloli masu mahimmanci tare da tabbatar da tsaro da kuma gudanar da ayyukan Makarantun

Advertisement

NIGERIAN TRACKER ta ruwaito cewa ana amfani da rufin ajujuwa wajen adana makamai.

A ranar 25 ga Janairu, 2024, ‘yan sanda sun kwato bindiga kirar AK-47 daga harabar, tare da harsashi masu yawa.

Advertisement

Bayan samun rahoton karshe da shawarwari, majalisar ta sake tura kwamitin ilimi domin ya binciki dalilin da ya sa gwamnatin jihar ba ta da masaniya kan halin da ake ciki.

An fahimci cewa daya daga cikin manyan batutuwan da suka addabi makarantun shi ne rashin zuwan dalibai Makarantun,

Advertisement

Kuma Makarantun dai na karkashin yakin Fagge ne, yayin da mafi yawan daliban sun fito ne daga yakin Nassarawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending