News
Farashin Man Girki Ya Yi Tashin Gauran Zabin Da Bai Taba Yi Ba A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rahotanni na nuni da cewa tashin farashin kayan abinci ya shafi kayan abinci irin su Man Garki da shinkafa da Taliya da hatsi da dankalin turawa da doya da rogo da dai sauransu.
Mafi akasarin masu sana’a da masu amfanin yau da Kullum a cikin gida da man girki a cikin birnin Kano sun daina Amfani da shi sosai saboda tsadar shi.
Wani bincike da Jaridar INDA RANKA ta gudanar a sassan birnin Kano da suka haɗa da Ungawa Uku ,Kurmawa, Naibawa, Tudun Yola, Tarauni da Hotoro ,Goron Dutse, Nasarawa, ya nuna cewa galibin masu amfani da man girki yanzu ya gagare sabida tsadar rayuwa.
A yanzu dai ana sayar da man Girki kwalba tsakanin Naira 2,800 zuwa Naira 3,100 , gwargwadon irin nau’in da ake samu a kasuwa.
Ana alaƙanta hauhawar farashin kayayyaki da faɗuwar darajar naira a Najeriya da kuma Rikicin gabas ta Tsakiya.
Jaridar INDA RANKA ta tattauna da wani kasuwar Singa wanda ke siyar da man Girki a kasuwar ya ce yanzu man Girki yana farawa ne daga Naira 86,000 zuwa 90,000
Janye tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi har yanzu yana ci gaba da yin tasiri ga tsadar kayayyaki.
Duk da masana sun yi hasashen za a iya samun sauƙi amma kayan abinci sun kara cirawa sama.
Amma masana na ganin sai gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don magance yiwuwar dorewar wannan yanayi na tsadar rayuwa a Najeriya
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
