News
Dokar Yancin Yara Bata Yarda A Gabatar Da Yara A Gaban Babbar Kotu — Lauya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kimanin masu zanga zangar su 76 ne aka tuhuma da manyan laifuffuka 10 da ya hada da cin amanar kasa, lalata kayayyaki, tada hankalin jama’a da bijire ma hukuma, kamar yadda yake kunshe a takardar tuhumar da kafar labarum Associated press tayi tozali da ita.
Kamar yadda takardar tuhumar ta nuna, shekarun yaran ya kama ne daga 14 zuwa 17 kacal da haihuwa.
Shugaba Tinubu Ya Yi Watsi Da Shawarwarin Da Aka Ba Shi Na Janye Sabon Kudirin Haraji
Bakinciki da takaici kan tsananin tsadar rayuwa a ya haifar da zanga zanga iri iri a yan watannin baya a Najeriya.
Akalla an kashe mutane 20 har lahira a watan Agusta, aka kuma garmake daruruwa a yayin wata zanga zanga da matasan kasar suka gudanar, inda suka nemi a sama musu, damarmaki da ya hada da samar musu ayyukan yi.
Wani lauya mai zaman kan shi dake zaune a Abuja babban birin Tarayya Abuja Akintayo Balogun, ya ce dokar yancin yara ba ta yarda asa yara fuskantar kaikomon shari’ar aikata laifi ba balle .
Don haka yace kuskure ne a gabatar da yara a gaban babbar kotun tarayya, sai fa har idan gwamnati ta babbatar cewa yaran sun haura shekaru 19 a duniya.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya Muyiwa Ogunjobi ya ce ana iya gurfanar da kowane mutum a kotun Nijeriya muddin shekarunsa ba su gaza bakwai ba.
Kotun ta tura manya daga cikin mutanen da ake tuhuma zuwa kurkuku, yayin da ta tura yaran zuwa wani gidan kula da kangararrun yara sai ranar 25 ga watan Janairu, inda za a ci gaba da shari’a.
Lauya Marshal Abubakar dake wakiltar wasu daga cikin yaran ya ce, kotu ta bayar da belin ko wane daya daga cikin yaran akan kudi Naira Miliyan 10 tare da aza musu matakai masu tsananin tsauri, da har yanzu suka gaza cikawa.
Abubakar ya kara da cewa, kasar da ta gaza ba yaran ta ilmi shine zata zabi ta hukunta wadannan yaran. Yaran dai sun kasance a tsare na tsawon kwanaki 90 ba tare da abinci ba.
Babban shugaban wata kungiyar fafutuka da karfafa shugabanci na gari a Najeriya, Yemi Adamolekun yace, ba abunda ya hada hukumomi da daure yara kanana.
Adamolekun ya kara da cewa, kamata yayi babbar mai shari’a ta Najeriya taji kunyar wannan lamarin a matsayin ta na mace kuma uwa.
Baya ga kasancewa daya daga cikin manyan masu samar da mai a Afrika, Najeriya na cigaba da kasancewa daya daga cikin matalautan kasashe a duniya. Cin hanci da rashawa da yayiwa kasar katutu ya zama abun ado ga jami’an gwamnatin kasar. Kwararru a fannin kiwon lafiya sun rika gudanar da zanga zanga akai akai don nuna rashin jin dadi da rashin gamsuwa kan dan abinda ake biyan su, da bai taka kara ya karya ba.
