Connect with us

News

 Yara 4 Sun Mutu Sakamakon Kulle Kan Su A Cikin Mota

Published

on

Yara 4 Sun Mutu Sakamakon Kulle Kan Su A Cikin Mota

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Akalla yara hudu ne suka mutu sakamakon shakewa bayan da suka kulle kan su a cikin mota yayin da suke wasa a Amreli da ke Gujarat a ranar Litinin kamar yanda Jaridar TIMES OF INDIA ta ruwaito.

Advertisement

Yan sanda sun ce wadanda lamarin ya rutsa da su, masu shekaru tsakanin 2 zuwa 7, sun kulle kan sune a cikin motar kuma sun mutu sakamakon shakewar da suka yi.

Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Sakin Yaran Da Aka Kama Yayin Zanga Zanga

A cewar ‘yan sanda, “Iyayen yaran sun tashi aiki ne a gonar Bharat Mandani da misalin karfe 7:30 na safe, inda suka bar ‘ya’yansu bakwai a baya, hudu daga cikin yaran sun shiga motar mai gonar, wacce ke kusa da gidansu.”

Advertisement

Lokacin da iyayensu da mai motar suka dawo da yamma, sai suka tarar da gawar yaran.

An yi rajistar mutuwar yaran a ofishin ‘yan sanda na Amreli kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending