News
Gwajin Ciwon Suga A Kai A Kai Ya Zama Dole Domin Cuta ce Mai Kisa a Boye
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta shawarci al’umma da su dinga yin gwajin Ciwon Suga kafin ta jawo wata babbar matsala ga jikunansu.
Kwamishinan Lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf, wanda Darakta mai kula da ayyukan likitoci Dakta Shehu Abdullahi ya wakilta, ne ya bayyana haka yayin wata bitar wayar da kai ta kwana daya da aka yi ma’aikatan gwamnati da aka zabo daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati game illoli da hanyar kare kai daga cutar.
Shugaba Tinubu Ya Gabatar Wa Majalisa Sabon Kasafin Kudin Shekarar 2025
Haka zalika, ya bayyana kokarin da gwamnatin Kano ke yi tare da hada hannu da sauran abokan huldarsu a sha’anin kula da lafiya domin dakile yaduwar cutar a Jihar.
Ya kara da cewa Gwamnatin Kano ta sahale a samar da wani sashi a ma’akatar lafiya da zai ringa kula lamarin ciwon suga da kuma sassan da ke kula da ciwon a dukannin asbitocin da ke fadin jihar.
A nasa jawabin na maraba, Daraktan sashin kula da dakile yaduwar cututtukan na ma’akatar, Dakta Ibrahim Aliyu Gano ya ce yin gwaji a kai a kai ya zama dole domin cutar ta zamo cuta da ke yin kisa a boye.
Yaduwar ciwon da kuma kula da mutane masu dauke da ciwon suga ya bayyana ta a matsayin wani abu mai daukar dogon lokaci wanda ake ganin sa ta wurin karuwar suga a cikin cikin jini.
Ya bayana cewa ana samun irin wannan sikarin daga abinci ne, musamman abinci mai sikari sosai, wanda jiki yakan farfasa a mayar da shi wani makamashi domin ba wa jiki karfi.
Ya lura cewa yin gwaji a kai a kai ya zama dole domin cutar ta zamo cuta da ke yin kisa a boye.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
