News
Shugaba Tinubu Ya Gabatar Wa Majalisa Sabon Kasafin Kudin Shekarar 2025
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gabatar da kudirin naira tiriliyan 47.9 a matsayin kudirin kasafin kudin shekarar 2025.
Ministan Kasafin Kudi da tsare tsare tattalin Arziki Alhaji Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis.
Kasafin kudin shekarar 2025 ya zone bayan taron majalisar zartarwa ta Ƙasa da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja.
Bagudu ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da tsarin kashe kudi na matsakaicin wa’adi wato (MTEF) na 2025-2027.
Minista Bugudu Ya ce gwamnati ta sanya ma’aunin gangar danyen mai a kan dala 75 kan kowace ganga da kuma samar da mai a kan ganga miliyan 2.06 kan tsarin Kasafin kudin.
Haka zalika ya kuma ce gwamnatin ta sanya farashin canjin dalar Amuruka a kan Naira 1,400 a yayin da gwamnatin ta kuma yi hasashen bunkasar kashi 6.4 cikin 100 na tsarin tatttalin arziki.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
