News
YANAYIN SANYI : Gwamnatin Kano Za Ta Samar Da Barguna Da Katifu Ga Wadanda Ake Tsare Da Su A Gidajen Gyaran Hali
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A nan kuma gwamnatin jihar Kano ta ba da tabbacin samarwa da wadanda ake tsare da su a gidajen gyaran hali barguna da katifu, duba da gabatowar yanayin sanyi.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugabar kwamitin yiwa daurarru afuwa ta jihar Kano hajiya Azimi Namadi bebeji yayin wata ziyarar aiki da ta kai hukumar da ke kula da gidajen gyaran halin.
Ta ce Gwamnatin Kano a shirye ta ke ta ba da gudunmawar ta a kowanne bangaren al’umma danganin ta sauke nauyin da ya ke kan ta.
Ta Kuma bukaci sauran al’umma musammam mawadata da su dinga taimakawa daurarrun, domin rage masu radadin da ke damun su
Hukumar da ke kula da gidajen gyaran halin ta ce kofar ta a bude ta ke ga duk mai san taimaka wa daurarrun a fadin jihar.