News
Za A Hana Yara Ƴan Ƙasa Da Shekara 16 Hawa Instagram da TikTok
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin Australia ta gabatar da ƙuduri domin samar da dokar da za ta haramta wa yara ƴan ƙasa da shekara 16 amfani da shafukan sada zumunta.
Ministar yaɗa labaran ƙasar, Michelle Rowland, ta shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewa wannan shi ne ƙuduri irinsa na farko da zai kare martabar yara da tarbiyyarsu a matakin da zai inganta ƙuruciyarsu kamar yanda BBC HAUSA ta ruwaito
Yadda Ƙananan Yara Suka Gudanar Da Zama A Majalisar Dokokin Kano
Ƙudurin zai buƘaci manhajoji kamar Instagram da TikTok, su tabbatar da bin dokar ko kuma su biya tarar miliyoyin daloli. Manhajojin na da sama da shekara guda domin fitar da tsarin yadda za su katange yara daga shiga shafukan nasu.
Sai dai haramcin bai shafi wasannin gametda yara ke yi a shafukan ba.
Sai dukkan majalisun Austraila sun amince da ƙudurin ne kafin zai zama doka.
