News
Dan Uwan Kwankwaso Ya Maka Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf A Gaban Kotu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rikicin fili a jihar Kano ya dauki sabon salo bayan da Garba Kwankwaso, kani ga tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ya maka Gwamnan Abba Kabir Yusuf a gaban Kotu
A cikin Shari’ar da Garba Kwankwaso ya shigar ya bukaci a shiga tsakaninsa da Gwamnatin Abba domin hana gwamnan daukar wani mataki akan wani fili da aka jima ana rikici akansa.
Jaridar Daily Nigeria ta rawaito cewa tun da fari asalin filin na Kwankwaso ne daya baiwa wani kamfani mai suna WAECO, amma sai tsohon gwamnan Abdullahi Ganduje ya kwace.
Daga baya sai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jiha ta tabbatar da kwace filin, wanda ya ke a unguwar Kwankwasiyya City., bisa hujjar cewa Kamfanin WAECO bashida wata cikakkiyar rijista.
Daga nan ne sai Ganduje ya dawo da kasuwar yan magani cikin wani bangare na filin kafin daga bisani a tashesu.
Itama sabuwar gwamnatin Abba da’ta zo sai taƙi maidawa kamfanin WAECO filin, shine Garba Kwankwaso ya shigar da kara a gaban Kotu.
A umarnin da ya bayar, Mai Shari’a Usman Na’abba ya bada umarnin hana taba filin ga gwamnati sannan ya dage sauraren koken zuwa 27 ga watan Nuwamba.
Cikin mutanan da Garba Kwankwaso ya shigar da Kara sun hadar da kwamishinan filaye da tsare-tsare na jihar Kano da Shugaban Hukumar Kula da tsare-tsare da cigaban Birane ta Jihar Kano, KNUPDA da Babban Lauyan Jihar Kano da mutun guda wanda ba’a bayyyanaba.
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
