News
Teburin Mai Shayi A Kano Na Fuskantar Barazanar Tabarbarewar Sakamakon Tsadar Rayuwa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Teburin Mai Shayi ya kasance muhimmin wuri ga samari da Dattawa da kuma tsofaffi da suke ganawa amma yanzu suna fuskantar barazana durkushiwa sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya
Rahotanni na nuni da cewa wadannan rumfunan kan hanya, da aka san su da siyar da shayi, burodi, indomie, da kwai, suna fama da raguwar abokan ciniki sakamakon karin farashi da ke barazanar durkushiwar kasuwancinsu jihar Kano .
Muhimmin Sako Zuwa Ga Gwamnonin Jihohin Arewa, Da Manyan Arewa Baki Daya!!!
Muhammad Sabiu Darma mai siyar da shayi a yankin TUKUNTAWA, ya bayyana yadda tattalin arzikin ya shafi kasuwancinsa. Ya ce, “A da, abubuwa suna tafiya daidai, amma yanzu muna fama. Duk abin da muke bukata ya yi tsada sosai.
Darma ya kara da cewa yanda ake sayen kayansa ya ragu sosai. “A da, nakan sayi mudu daya da rabi na sukari; amma yanzu sai rabi kawai.
A kullum ina siyan kwali uku na kwai, yanzu kuwa rabin kwali ƙwai na ke siya kawai. Har ma indomie, da na saba siyan kwali biyu a kullum, yanzu rabin kati kawai nake iya siya.”
Farashin kofin shayi ya karu daga N50 zuwa tsakanin N150 da N200, yayin da indomie da kwai suka zama abin da mafi yawan abokan ciniki ba za su iya saya ba.
Ya ce, “Idan abokin ciniki da ya saba cin kwai uku, indomie biyu, da shayi da madara bai iya siyan rabin abun da ya siya ba, to ka san akwai matsala.”
Wani Abokan cinikin yau da kulkum a wurin shayi bayyana irin kalubalen da suke fuskanta ya ce, “A da, ina sha shayi da madara, burodi, da butter, indomie da kwai. Amma yanzu, shayi mara madara kawai da burodi mara komai nake iya saya. Karshen lokacin da na ci indomie tun watanni biyu da suka wuce.”
Haka zalika shima wani abokin ciniki, ya ce yanzu yana cin Taliya maimakon indomie. “Na rage cin indomie daya da kwai biyu, amma yanzu ma ba zan iya saya ba sakamakon tsadar rayuwa. Yawancin masu shayi yanzu suna dafawa Taliya da wake saboda tafi sauki.
Direban Adaidaita Sahu ya ce, “A da, ina cin indomie da kwai da safiya da dare, amma yanzu Taliya kawai nake ci a wasu lokutan. Rayuwa ta yi tsada.”
Sai dai masu shayi suna gyara abincin da suke bayarwa, suna ba da wasu zaɓuɓɓuka masu rahusa kamar Taliya da wake, amma tsadar kayan abinci na ci gaba da zama babban kalubale ga kasuwancinsu.
Kasuwancin shayi, wanda a da ya kasance tushen samun kudin shiga mai kyau da kuma zaɓi na yau da kullum ga yawancin ‘yan Najeriya, yanzu matsalolin tattalin arziki da Tsadar Rayuwa yasa masu sana’a da kuma abokan cinikinsu ke fuskanta cikin wani hali.
