Politics
Babbban Jigo A Jam’iyyar Labour party Ya Sauya Shega Zuwa Jam’iyya Mai Mulki Ta APC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jam’iyyar Labour Party (LP) na fuskantar barazana sakamakon fucewar zababbbin shuwagabanninta zuwa babbar Jam’iyya mai mulki ta Ƙasa All Progressives Congress wato (APC).
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a safiyar Yau Talata aka samu labarin sauya shekar Ms Dalyop Chollom dan majalisa dake wakiltar mazabar Bdaga da dLadi/Riyom ta Jihar Filato dake shugabanci a Jam’iyyar labour party (Lp)
Shugaban majalisar wakilai , Abbas Tajuddeen Abbas ne ya sanar da sauya shekar Dalyop wadda aka karanta a zauren majalisar.
Da yake sanar da sauya shekar, shugaban majalisar ya ce dan majalisar ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar LP zuwa APC ne bayan ya yi tunani mai zurfi da kuma sakamakon rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a fadin Kasar.
Ya ce makomar siyasar al’ummar mazabar sa tana nan kuma ya yi imanin cewa zai yi wa al’ummarsa hidima sosai a jam’iyya mai mulki kamar Yadda yakeyi a baya.
Abbas Tajudden Abbas wanda shine shugaban majalisssar wakilai ya bayyyana fucewar Dan majalisssar daga Jam’iyyar LP zuwa APC a matsayain cigaba ga Jam’iyyar su da kuma yabo da Al’ummar Nageriya keyi mata.
