News
Sai Tsohon Kayan Mu Ya Kare Zamu Rage Farashin Man Fetur — Kungiyar IPMAN
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ƙungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN da kuma kamfanin man fetur NNPCL , sun ce za su ci gaba da sayar da man fetur a tsohon farashi har zuwa lokacin da tsohon kayan da suke da shi zai ƙare.
Kamfanin na NNPCL dai ya ce a sabon farashin zai riƙa bai wa dillalan, man kan naira 899 inda su kuma za su sayar a kan naira 935.
Bana Goyon Bayan Kayyaɗe Farashin Kayayyaki – Shugaba Tinubu
Ƙungiyar dillalan man ta ce a yanzu haka tana ci gaba da tattaunawa da matatar Dangote domin ganin yadda za su soma ɗaukar man a sabon farashin, kamar Alhaji Salisu Ten-Ten, shugaban dillalan na shiyyar arewa maso yamma ya bayyanawa BBC.
Idan za’a iya tunawa dai a makon daya gabata ne kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN tace za’a fara siyan man fetur a farashin naira 935 daga ranar litinin data gabata.
Sai dai hakan bai kasance ba yayin da aka rika siyan man akan farashin naira dubu sa naira 70, zuwa da naira 80.
Amma daga baya NNPC ya rage farashin zuwa 935, a birnin tarayya Abuja.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
