News
DMCSA Za Ta Hada Hannu Da NDLEA Don Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano DMCSA ta nemi hadin kan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA reshen Jihar Kano don yakar mummunar ta’adar nan ta ta’ammaali da miyagun kwayoyi, musamman a tsakanin ma’aikatan gwamnati.
Shugaban Hukumar Samar da Magunguna ta Jiha, Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar aiki zuwa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi da ke nan Kano a safiyar Litinin din nan.
Sai Tsohon Kayan Mu Ya Kare Zamu Rage Farashin Man Fetur — Kungiyar IPMAN
Famasist Gali Sule ya nuna damuwarsa sakamakon yanda shan miyagun kwayoyi ya zama ruwan dare, musamman a tsakanin matasa, a fadin jihar nan.
Shugaban ya ce za su yi wa dukkanin ma’aikatan hukumar, ciki har da shugannin ma’aikatar, gwajin shan miyagun domin tabbatar da da’a.
Haka zalika, hukumar za ta shirya taron wayar da kai a kan illar shan miyagun kwayoyi, in ji shi.
Da yake jawabi, Kwamandan hukumar ta NDLEA reshen jihar Kano Abubakar Idris Ahmad, wanda ya sami wakilcin Mukaddashin Kwamanda Yaya Muhammad Aminu, ya ce ma’aikatarsa a shirye take domin hada kai da Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar Kano domin yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
