Connect with us

News

Gwamna Fintiri Ya Sanar Da Kirkirar Sabbin Masarautu 7 A Adamawa

Published

on

Gwamna Fintiri Ya Sanar Da Kirkirar Sabbin Masarautu 7 A Adamawa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamna jihar Adamawa Ahmadu Fintiri na ya sanar da kirkirar sabbin masarautu domin samar da zaman lafiya da kuma hadin kai da gwamnati ga yankunan jihar.

Gwamna Fintiri ya sanar da hakan ne a jawabin karshen shekara da yayi a Yola ranar Litinin.

DMCSA Za Ta Hada Hannu Da NDLEA Don Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi A Kano

Masarautun sune; Hoba, wato Hong mai daraja ta biyu; Madagali (Gulak mai daraja ta biyu); Michika (Michika, daraja ta biyu); Fufore (Fufore daraja ta biyu); Gombi (Gombi, daraja ta uku); Maiha (Maiha, daraja ta uku); Yungur (Dumne, daraja ta uku),” kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafin X ranar Litinin.

Ya ce gyare-gyaren za su taimaka wajen inganta harkokin gwamnati da ƙarfafa masarautun gargajiya don amfanin jihar da al’ummarta.

Ya ƙara da cewa masarautun gargajiya suna matuƙar taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya acikin al’umma don haka ne halin tsaro ya ke cigaba da ingantaa jihar.

Advertisement

 

 

 

PRIME TIME NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending