News
Jami’an Hukumar Kwastam Sun Kama Tirela 82 Makare Da Shinkafar Waje
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Jami’an Hukumar Kwastom sun sanar da kama jaka 48,912 na shinkafar waje da aka shigo da ita cikin ƙasar tsakanin Janairu da Disamba 2024.
Shugaban Kwastom (CAC) na sashen, Compt. Kola Oladeji, ne ya baiyyana hakan a cikin wata ganawa da manema labarai a ranar Talata, ya bayyana cewa shinkafar da aka kama ta kai Tirela 82.
Gwamna Fintiri Ya Sanar Da Kirkirar Sabbin Masarautu 7 A Adamawa
A cewar Oladeji, sashen ya kuma dakatar da wasu kayan haraji guda 707 da suka hada da wani jimillar Kudaden Haraji na Naira biliyan 18.71.
Haka zalika ya bayyana wasu kayan kamar Lita 191,975 na man fetur; Kilogram 7,861 na Cannabis sativa; Kayan fatar Jaki guda 6,168; Lita 37,630 na Tramadol da motocin 207,
Sauran kayan da aka kama sun hada da: Kartons 6,755 na kayan abincin kaza na waje, Bales 1,433 na tufafin da aka yi amfani da su, motoci 1,773 na firij din da aka yi amfani da su da kartons 317 na magungunan haram.
Sashen ya kuma kama mutane 94,
