Connect with us

News

Da Yiwuwar Kamfanonin Sadarwa Su Kara Kudin Kiran Waya Da Na ‘Data’ A Farkon Shekarar 2025

Published

on

Da Yiwuwar Kamfanonin Sadarwa Su Kara Kudin Kiran Waya Da Na 'Data' A Farkon Shekarar 2025

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Akwai yiwuwar kamfanoni sadarwa za su ƙara kuɗin kira da na data da kuma tura rubutaccen saƙo a farkon shekarar 2025 mai kamawa.

Wani babban jami’in wani kamfanin da sadarwa ya bayyana cewa kamfanonin suna da ƙwarin gwiwar samun sahalewar Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) domin kara kuɗin kira da na data.

Advertisement

Rayuwar Muhammad Garba

Jami’in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa kamfanonin sadarwar na MTN da Airtel da 9Mobile sun riga sun aika wa NCC da buƙatarsu kuma bisa dukkan alamu suna ganin haske.

Idan suna samu Hukumar NCC ta amince, buƙatar kamfanonin sadarwar na ƙarin kuɗin da suka shafe kusan shekara goma suna nema, ta biya ke nan.

Advertisement

Hukumar NCC ta ƙi amince wa kamfanonin ƙara kuɗi tun a zamanin tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami.

Kimanin shekara 10 ke nan yanzu kamfanonin suke neman ƙara kuɗi kira da na data da tura saƙonni, bisa dalilin hauhawar farashin kayayyaki, amma gwamnati tana ƙin ba su damar yin hakan.

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending