News
Aƙalla Mutum 71 Ne Suka Rasu Ya Yin Da Babbar Mota Cike Da Fasinjoji ‘Yan Biki Ta Kife Cikin Kogi
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Aƙalla mutum 71 ne suka rasu a Ethiopia a lokacin da wata babbar mota cike da fasinjoji ta faɗa a cikin kogi, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin yankin Sidama da ke kudancin ƙasar ya tabbatar.
Hatsarin wanda ya laƙume rayukan maza 68 da mata uku, ya faru ne a ranar Lahadi a gundumar Bona, kamar yadda sanarwar da aka fitar ranar Lahadi da dare ta bayyana.
Akalla Kaso 53.9 Cikin 100 Na Yara A Najeriya Na Fama Da Tsananin Fatara Da Yunwa – Rahoto
Wosenyeleh Simion, wanda shi ne mai magana da yawun gwamnatin yankin Sidama ya bayyana cewa fasinjojin baƙi ne waɗanda za su je wurin biki, inda wasu iyalan suka rasa mutane da dama.
Shi ma gidan talabijin na Ethiopia EBC ya ruwaito cewa fasinjojin suna hanyar zuwa wuri biki a lokacin da hatsarin ya faru.
