Connect with us

News

Buguwa Ya Yin Tuki Ya Haddasa Konewar Gidaje 4 A Jigawa

Published

on

Buguwa Ya Yin Tuki Ya Haddasa Konewar Gidaje 4 A Jigawa

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa sun tabbatar da cewa a ranar Lahadi da misalin karfe 12 :30 dare a Unguwar Elpies Street, Mobile Quarters Dutse, wani Muhammad Galadima ‘m’ mai shekaru 32 da kuma Abdullahi Abubakar Sadiq mai shekaru 41 da haihuwa , wanda ake zargi da shan barasa, tare da tuka mota kirar Toyota ya kutsa cikin wani gida , ya ruguje bangon ya wuce kai tsaye zuwa falo inda matar da ‘ya’yanta ke barci.

Advertisement

A dalilin haka ne motar da gidan gaba daya ta kone kurmus, wanda ya shafi wasu gidaje uku da ke makwabtaka da su wadanda suma suka kone kurmus.

Jami’an Hukumar DSS sun kama Mahdi Shehu

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam ya bayyana haka a wata sanarwa da ya turawa Jaridar JUSTICE WATCH NEWS

Advertisement

Ya ce bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sanda sun yi tururuwa zuwa wurin, inda aka kashe gobarar sakamakon hadakar ‘yan kwana-kwana da samari nagari.

Ya bayyana cewa, “Duk wadanda ake zargin da kuma motar an tsare su domin gudanar da bincike mai zurfi.

Advertisement

“Bayan kammala cikakken bincike, za a gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a gaban kuliya.”inji Shi

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending