News
Gwamnatin Kano Ta Ci Alwashin Kawo Karshen Wurare Da Ake Tara Sharar Ba Bisa Ka’ida Ba A Jihar
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin jihar Kano ta koddari aniyar kawo karshen yawaitar tara shara akan tituna da wasu wurare da ake tara sharar ba bisa ka’ida ba a jihar
Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano wacce zata jagoranci wannan shiri da hadin guiwar ma’aikatar sufuri da ta kasuwancita jihar.
Sojojin Nijeriya sun tarwatsa sansanin Bello Turji, sun kashe ‘yan ta’adda 25 a Zamfara
Kwamishinan Muhalli da sauyin yanayi na jihar Dr.Dahiru Muhammad Hashim ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da shirin kawar da shara da sarrafata shirin da aka kaddamar a kasuwar Kantin Kwari ranar Litinin.
Kwamishinan yace a yanzu haka an dawo da yawancin ma’aikatan shara da aka daina gani a baya zuwa kan tituna da wuraren da ake tara shara a birnin Kano domin tabbatar da shirin.
An kaddamar da fara aikin kwashe sharar ne a kasuwar Kantin Kwari kan titin IBB,Kuma acewar kwamishinan daga litinin din nan za’a daina ganin tilin shara akan titunan Kano
