Connect with us

News

Al,umma Na Takaicin Yadda Masu Gidajen Burodi Suka Ki Saukar Da Farashi Kayansu Duk Da Fulawar Ta Sauka

Published

on

NAFDAC ta gargaɗi masu burodi kan daina amfani da wasu sinadarai 2 wajen yin burodinsu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƴan kasuwar Singa da ke nan Kano, ta nuna takaicinta game da yadda masu Siyar da Buredi da sauran masu harka da Fulawa suka kasa sassautawa mutane, duba da yadda farashin Buhun Fulawa ke ci gaba da faduwa yanzu haka a kasuwanni.

Advertisement

Shugaban ƙungiyar Barista Junaid Muhammad, shi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Gidan Radiyon Dala FM, yayin da yake bayani kan irin rawar da suke takawa wajen ganin an samu saukin kayayyakin da ‘yan kasuwarsu suke siyarwa mutane a jihar Kano.

‎Karancin Gado A Asibitin Murtala Muhammad Na Haifar Da Barazana Ga Marasa lafiya ‎ ‎—Bincike

Barista Junaid ya kuma ce babban abin takaicin shi ne yadda a baya da farashin kowanne buhun Fulawa ɗaya ya yi tashin gwauron zabi zuwa Naira dubu 80, amma kuma a yanzu da farashin ta ya sauko zuwa dubu 60, masu ta’ammali da ita suka gaza rage farashin su kamar masu Burodi da kuma Gurasa da sauransu

Advertisement

Ya kuma ce suna nan suna kokarin ganin sun samar da banki na kasuwa musamman ma domin ganin suna tafiya da zamani

Sai dai daga ɓangaren sa shugaban ƙungiyar masu gidajen Burodi na jihar Kano Alhaji Jibril Abubakar Hamza ya musanta zargin da ake yiwa masu gidajen Burodin kan cewar farashin fulawar ya sauka amma sun gaza sauke farashin Burodi.

Advertisement

Ya kuma ce akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta shigo ciki lamarin wajen wadata Alkama a ƙasar nan, domin ƙara samar da Fulawa ga ƴan kasuwa ta yadda za’a ƙara samun sauƙin al’amura.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending