News
ALLURAR FIZER : Gwamnatin Tarayya Da Gwamnati Kano Ya Kamata Su Biya Diyyar Wanda Suka Nakasa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An bukaci Gwamnatin Tarayyya da Gwamnatin Jihar Kano dasu biya wadanda allurar fizer ta illata hakkokin su, yadda ya kamata ba tare da kunbi-kunbiya ko zaluntarsuba.
Mataimakin shugaban kungiyar masu neman hakkin su sakamakon illar da allurar Pizer ta yi masu mai suna Sharif Sunusi Abubakar ne ya bukaci hakan yayin wani taro da suka yi da hadin gwiwa da gidan talabojin na NEWS CENTRAl a jiya Alhamis a Jihar Kano.
Ya ce akwai bukatar mahukunta da masu ruwa da tsaki a jihar Kano su tsaya kai da fata wajen ganin an kowa hanyoyin da da za’a taimaka a biyar dukkaknin hakkkokin wadan da wanda alluara ta shafa.
Anasa jawabin shima daraktan gidan talabijin na News Central, Kayode Akintemi Wanda Salisu Ibrahim ya Yi bayani a madadin sa ya ce sun shirya taron ne da nufin taimakawa wadanda rayuwar su ta nakasa sanadiyar wannnan allurar ta fizer.
Ya awaki bukatar irinsu da dama da ya kamata ace sun taimaki Al’umma domin ganin rayuwarsu ta cigaba da ingantuwa.
Suma wasu daga cikin wadanda abun ya shafa Bilkisu Sa’id Abbas da Rukayya Salisu, cewa suka yi allurar ta fizer ta mayar da rayuwar su baya a dan haka suke bukatar daukin mahukumta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tun a shekarar 1996 kamfanin ya yi gwajin allurar a nan Kano in da al’umma da dama suka nakasa wasu kuma suka rasa rayukan su tun a lokacin.
Haka zalika a shekarar 2009, kamfanin Pfizer ya cimma matsaya da gwamnatin jihar Kano, inda aka amince da biyan dala 175,000 ga duk wanda ya nakasa. Sai dai, tambayoyi sun taso game da rabon wadannan kudade da kuma rawar da gwamnati ke takawa wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
