News
Ba Mu Muka Kar Zomon Ba —Shugaba Tinubu Ga Sarki Sunusi
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Gwamnatin Tarayya ta ce, ba fa ita ce ta kar Zamon ba, domin kuwa ko ratayar ma ba a bata ba.
A cewar gwamnatin Shugaba Tinubu ita ba ta ma bukatar shawara daga wajen Sarkin na Kano na 16 Muhammadu Sunusi ll.
Babbar Mota Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 9 Har Cikin Gidan Su
A cikin wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kakakin gwamnatin tarraya kuma ministan yada labarai Muhammad Idris, ya cegwamnatin tarraya ba ta bukatar shawara daga wajen Sarki Sunusi domin tana da kwararrun masu ba ta shawara kan tattalin arziki.
“Kamar yadda ka ce mutanen cikin gwamnatin nan abokanka ne, amma tun da sun yi maka rashin kirki kaima za ka rama, to gara kasancewa fa mu ba mune muka kar zomon ba” inji sanarwar.
Rahotanni na nuni da cewa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ll yace Mutanen da ke cikin Gwamnantin nan na Tinubu duk abokai nane, amma tun da sun ya dani, nima na ya dasu, ba zan taba basu shawara don su samu nasarar magance matsalar tattalin arzikin Najeriya ba
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
