News
Ya Kamata Sabuwar Gwamnati Ta Dauki Darasi Daga Kura-Kuran Da Gwamnatocin Baya Suka Tafka—-sunusi na biyu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya shawarci gwamnati mai jiran gado da ta dauki darasi daga kura-kuran gwamnatocin da suka shude suka yi, ta hanyar nada kwararrun mutane a mukamai da za su bunkasa cigaban kasa.
Da yake jawabi a yayin taron kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Talata, Malam Muhammadu Sanusi ya ce yana fatan ganin jerin sunayen ministocin da shugaban kasa mai jiran gado zai nada.
Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Mutu a Kano Sakamakon Shan Shayin Zaƙami a Wurin Biki
Ya kuma yi kira ga gwamnati mai zuwa da ta kare hukumomin gwamnatin kasar daga abunda ya baiyana na ‘Yan Siyasa masu wuce gona da iri.
Advertisements
