News
Kano Pillars Ta Dakatar Da Kocinta Usman Abdullah Na Tsawon Makonni Uku
DAGA UMAR ABDULLAHI HOTORO
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta dakatar da Kocinta Usman Abdalla, tsawon makonni uku, sakamakon rashin ƙoƙari da kuma nuna halayyar da bata kamata ba ga magoya bayan ƙungiyar.
Kungiyar ta ɗauki wannan matakin ne bayan tashi daga wasan da ta buga canjaras (0-0) da Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha a ranar Lahadi 2-02-2925.
Dakatarwar ta biyo bayan rashin tabuka abin a zo a gani a baya bayan nan, da kuma harzika magoya bayan kungiyar, bayan tashi daga wasan da Kano Pillars din ta buga chanjaras da Bayelsa United a filin wasa ana Sani Abacha dake Kano.
Ƙungiyar dai tana fama da rashin nasara a ƴan kwanakin nan inda a cikin wasanni uku wasa ɗaya kawai ta samu nasara a kai.
Bayan tashi daga wasan ne magoya bayan ƙungiyar suka yi wa Usman Abdalla ihu, kamar yadda rahotanni suka bayyana, lamarin da bai yi wa mai koyarwar daɗi ba shi kuma ya mayar da martani.
Cikin wata Sanarwar da Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Alhaji Ali na Yara Maisamba ya sanyawa hannu ta ce, mataimakin mai horaswar Tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Ahmad Garba Yaro-Yaro, shi ne zai ci gaba da jagoranci ƙungiyar a matsayin riƙon ƙwarya tare da taimakon Abubakar Musa da tsohon ɗan wasa Gambo Muhammad da Sulaiman Shua’aibu da kuma Ayuba Musa
