Connect with us

News

Za Mu Ci Gaba Da Yin Hadin Gwiwa Da Kungiyoyin Masu Zaman Kansu Don Inganta Rayuwar Matasa — Gwamnatin Kano 

Published

on

IMG 20250208 WA0016

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Jihar Kano ta sake nanata kudirinta na cika alkawurran da ta dauka lokacin kamfe, musamman wajen koyar da matasa da mata sana’o’i, samar da ayyukan yi, da kuma inganta ilimi, musamman ga masu bukata ta musamman.

Advertisement

Wannan ya bayyana ne ta bakin Babban Mai taimakawa Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf kan harkokin matasa da wasanni, Sani Musa Danja, a yayin wata ziyara da ya kai cibiyar koyar da matasa sana’o’i. Cibiyar dai tana karkashin shirin da Kungiyar 9ja Food Fiesta ta shirya, tare da hadin gwiwar ofishin Babban Mai baiwa Gwamnan shawara kan harkokin matasa da wasanni.

Wani Bangare Na NNPP Ya Kori Kwankwaso Da Buba Galadima Daga Cikin Jami’yyar 

Sani Musa Danja ya jaddada cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta mayar da hankali wajen kula da masu bukata ta musamman, domin tabbatar da cewa suna cin gajiyar duk wani shiri na cigaba ko tallafi da jari. Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta dauki nauyin karatunsu da kuma tabbatar da cewa suna da cikakkiyar damarsu kamar kowa wajen samun tallafin da zai inganta rayuwarsu.

Advertisement

Shugaban ƙungiyar 9ja Food Fiesta, Muhammad Mustapha, ya bayyana cewa sun zo jihar Kano da nufin koyawa matasa maza da mata 2,000 sana’o’i, amma daga bisani suka fahimci cewa akwai bukatar ƙara yawan mahalarta zuwa 3,000.

“Babu shakka, wannan aiki ne domin tallafawa rayuwar matasan jihar Kano, kamar yadda muka yi a Abuja. Muna matuƙar jin daɗin yadda mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan harkokin matasa da wasanni, Sani Musa Danja, ya ba mu duk wata gudunmawa da muke bukata domin tabbatar da nasarar shirin da muka sanya a gaba.”

Advertisement

Haka kuma, Muhammad Mustapha ya yi kira ga kamfanoni da masu hannu da shuni a jihar Kano da su shiga cikin shirin, domin tallafawa matasan da suka kammala koyon sana’o’i da jari ko kayan aiki, domin su samu damar dogaro da kansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending